An dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zamba

An dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zamba

- Rahotanni sun kawo cewa an dakatar da shugaban hukumar bada inshorar kiwon lafiya ta kasa wato NHIS

- Akwai rade-radin cewa dakatar da Usman Yusuf da na da alaka da laifin aikata zamba

- Ministan lafiya, Isaac Adewole ne ya sanya hannu a dakardawan a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli

Ministan kiwon lafiya, Isaac Adewale ya dakatar da Usman Yusuf sakataren hukumar bada inshorar kiwon lafiya ta Kasa wato NHIS.

An rahoto cewa an sanya hannu a dakatarwan ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli wanda ya fara aiki a take, kusan shekara daya bayan gwanin a harkar lafiya mai shekaru 54 ya fara aiki a hukumar ta bada inshorar kiwon lafiya a ranar 29 ga watan Yuli, 2016.

Ko da daiUsman Yusuf ya karyata al’amarin dakatarwar inda ya bayyana cewa ba’a dakatar dashi ba. Majiyar mu ta sanar da mu cewa tunda yammacin ranar Alhamis din ne Usman Yusuf ya amshi takardar dakatarwarsa.

An dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zamba

An dakatar da Shugaban hukumar NHIS, kan zargin aikata zamba

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

Ana tuhumar Usman Yusuf da yin amfani da wasu kudade da ya kai naira Miliya 200 don gudanar da tirenin ga wasu ma’aikatan hukumar da kuma rashin jituwa dake tsakaninsa da ministan kiwon lafiya Isaac Adewale.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel