Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

- Gwamnan jihar Sakkwato yayi rashin mahaifiya

- An yi jana'izar Hajiya Fatima Dammu a ranar Alhamis

A ranar Alhamis 6 ga watan Yuli ne gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal yayi rashin mahaifiyarsa Hajiya Fatima Dammu a garin Tambuwal dake karamar hukumar Tambuwal na jihar.

Wani ma’abocin kafar sadarwa na Facebook, Bello Danfulani ne ya bayyana hakan a shafinsa, inda ya daura hotunan jana’izar marigayiya Hajiya Fatima.

KU KARANTA: An yi bikin buɗe sabon ofishin hukumar EFCC na jihar Kaduna (HOTUNA)

Majiyar NAIJ.com ya bayyana cewar marigayiyar ta rasu ta bar yaya guda bakwai, daga ciki akwai gwamnan jihar da kuma Nura Ibrahim, Turakin Tambuwal na hukumar kwastam.

Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

Jana'izar

Wasu da suka halarci sallar jana’izar Hajiya Fatima sun hada da gwamnan Tambuwal, Mataimakin gwamna Ahmad Aliyu, Sakataren gwamnati Farfesa Bashir, kwamishinoni da sauran masu fada a ji a jihar.

Gwamnatin jihar Sakkwato tayi babban rashi – KARANTA

Yayin jana'izar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda harsashi ya kuskure wani matashi, ya mutu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel