Buhari: Wani gwamnan arewa ya bada hutun kwana 1 don a yi ma shugaba Buhari addu’a

Buhari: Wani gwamnan arewa ya bada hutun kwana 1 don a yi ma shugaba Buhari addu’a

- Ma’aikatar jihar Jigawa sun samu hutun kwana daya domin su taya shugaban kasa addu’an samu lafiya

- Majalisar zartarwar jihar ta yanke shawarar a zaman ta a ranar Laraba

-An sa ran cewa za a yi ma marigayi Danmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule addu’a Allah ya sa Jannatul Firdausi ne makomarsa

Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana ranar juma'a,7 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu ga ma’aikatar jihar don a yi ma shugaban kasar Muhammadu Buhari addu’a na musamman a kan kiwon lafiyar shugaban.

Jami'in hulda da jama'a a ofishin shugaban ma’aikatar jihar, Alhaji Isma'il Ibrahim ya sanar da wannan a cikin wata sanarwa a Dutse a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni.

Ibrahim ya bayyana cewa, majalisar zartarwar jihar ne ta yanke wannan shawarar a zaman ta a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli.

Buhari: Wani gwamna arewa ya bada hutun kwana 1 don a yi ma shugaba Buhari addu’a

Shugaban kasar Muhammadu Buhari

Ya bayyana cewa, gwamnatin ta ayyana ranar juma'a a matsayin ranar hutu domin ma’aikatar jihar su samu daman yi ma shugaban kasar Muhammadu Buhari addu’o’i.

KU KARANTA: Fr. Mbaka ya saki bam a kan lafiyar Buhari, ya ce ya ji kuka daga Aso rock

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, a wannan rana, an sa ran cewa duk ma’aikata da dukan al'ummar jihar za su yi addu'a ga Allah Madaukaki ya ba shugaba Buhari lafiya ya kuma dawo da shi kasar lafiya.

Haka kuma ana sa ran cewa za su kuma yi addu'a ga Allah Madaukaki a kan marigayi Danmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule cewa Allah ya sa Jannatul Firdausi ne makomarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel