Obasanjo zai mutu sannan Najeriya zata ga inda karfinmu ya kai – Nnamdi Kanu

Obasanjo zai mutu sannan Najeriya zata ga inda karfinmu ya kai – Nnamdi Kanu

- Shugaban kungiyar IPOB, ya dau zafi kan furucin da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi

- Kanu ya ce tsohon shugaban kasar zai mutu kan cewa da ya yi yan Najeriya su dakatar gga kira ga neman Biyafara

- Shugaban masu fafutukar neman Biyafara y a ce shi da mutanen na son ficewa daga Najeriya

A ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, shugaban kungiyar masu fafutukar neman yankin Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu, ya ce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo zai mutu kan cewa da ya yi ya zama dole a dakatar da shi da masu kira ga Biyafara.

Ya ce tsohon shugaban kasar zai mutu kan furta wadannan kalai don su san irin karfi da mutanen Biyafara ke da shi.

Shugaban kungiyar ta IPOB ya bayyana hakan a martanin sag a furucin Obasanjo kan cewa dole ýan Najeriya suyi duk abunda zasu iya don dakatar da kiran Biyafara da Kanu ke jagoranta.

Obasanjo zai mutu sannan Najeriya zata ga inda karfinmu ya kai – Nnamdi Kanu

Obasanjo zai mutu sannan Najeriya zata ga inda karfinmu ya kai inji Nnamdi Kanu

A wani bidiyo da NAIJ.com ta samu, Kanu ya ce shi da mutanensa bazasu taba rushewa ba sannan kuma babu wanda ya isa ya hana su cimma Biyafara.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda karamin yaro ke bin bola don neman abunda zai ci (hotuna)

Ya kuma ce Obasanjo ya yi tambayoyi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin ya furta zancen banza akan su, ya kara da cewa a gidan namun daji ne kawai ake samun tsofaffin mutane da basa ritaya ta girma da arziki.

Kalli bidiyon a kasa:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel