Wani babban kwamishinan APC ya yi murabus

Wani babban kwamishinan APC ya yi murabus

- Wani kwamishina a jihar Oyo ya yi murabus daga majalisar zartarwar jihar

- Kwamishinan ya sanar da ajiye aikin ne ta hanyar sadarwa a shafinsa ta Facebook

- Har yanzu ba a bada dalilin da yasa ya ajiye aikin ba

Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Oyo, Mista Mudashiru Abdulganiyu ya yi murabus daga gwamnatin gwamna Abiola Ajimobi.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, tsohon kwamishinan ya yi wannan sanarwar ne a ranar Talata, 4 ga watan Yuli da yamma, ta hanyar sadarwa a shafinsa ta Facebook 'Muda Ganiyu'.

Abdulganiyu ya rubuta a shafinsa ta Facebook cewa: "Alhamdulillah! Alhamdulillah !! Alhamdulillahi Rabil-Alameen”.

Wani babban kwamishinan APC ya yi murabus

Gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi Source: dailypost.ng

Ya ku masu kaunata, ina so ne in sanar da ku cewa na ajiye aiki na a matsayin kwamishinan ayyuka na musamman. Na gode da addu’o’in ku. Allah ya albarkace ku gaba daya".

KU KARANTA: Siyasa: Fiye da matasa 100 suka yi sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kogi

Tsohon kwamishinan bai bayyana dalilin da yasa ya ajiye aikin ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel