Abubuwa 4 da Saraki ya tattauna tare da na kewaye da Aso Rock a kasar Saudiyya

Abubuwa 4 da Saraki ya tattauna tare da na kewaye da Aso Rock a kasar Saudiyya

A ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli, an gabatar da wani umurni, cewa majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Saraki, ya zamo mukaddashin shugaban kasar jumhuriyyar Najeriya.

NAIJ.com ta rahoto cewa sanatan dake wakiltan Abia ta kydy, Eyinanya Abaribe, ya daukaka wani kara na cewa kasar bata da shugaban kasa ko mukaddashin shugaban kasa a halin yanzu, inda ya kara da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi kamar babu su ne a kasar a yanzu.

Sahara Reporters ta rahoto cewa anyi zargin wata kungiya da Saraki ke jagoranta da kuma kungiyar Aso rock karkashin jagorancin Isa Funtua sun hadu a Saudiyya don tattauna yadda zasu kwace fadar shugaban kasa daga mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

A cewar rahoton da ba’a tabbatar ba kungiyar shugaban majalisar dattawa sun hada da Ahmadu Adamu Mu’azu, wani tsohon gwamnan jihar Bauchi da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, da kuma Bala Mohammed, wani tsohon ministan babban birnin tarayya wanda ke fuskantar tuhuma na sadar kudi.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda karamin yaro ke bin bola don neman abunda zai ci (hotuna)

Ga abubuwan da aka ce sun tattauna a kai a kasa:

1. Yadda za’a tsige mukaddashin shugaban kasa Osinbajo daga mulki ta karfi, sun ce suna iya dawo da shugaban kasa Buhari Najeriya a duk halin da lafiyarsa ke ciki.

2. An kum yi zargin cewa sun tattauna kan hanyar da zasu sa shugaba Buhari ya yi murabus sannan su tursasa Osinbajo amincewa da alkalin alkalai na tarayya, Abubakar Malami a matsayin mataimakin shugaban kasa.

3. Bugu da kari, za’a tursasa Osinbajo cire Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC.

4. Daga karshe na kewayen zasu haddasa rikicin siyasa dadama a kasar wanda zai tunzura sojoji su karbi mulki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel