Patience Jonathan tace gwamnatin Buhari na cin zarafinta, ta kai wa majalisa kara

Patience Jonathan tace gwamnatin Buhari na cin zarafinta, ta kai wa majalisa kara

-Uwargida Patience Jonathan ta zargi wasu hukumomin tsaro da cin zarafin ta

-Dan majalisa mai wakiltan yankin Okrika ne ya gabatar da takardan koken a gaban majalisan

-Uwargida Patience ta nemi a sassauta mata saboda irin aikin sadaukar da kai da maigidan ta yayi

Uwargidan tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, Uwargida Patience Jonathan ta zargi hukumomin tsaro da cin zarafi da musguna mata da iyalen ta, kuma tana neman majilissan wakilai na kasa ta shiga tsakanin su.

A wata takardan koke da ta aike ma majalisan, Uwargidan tana rokon majalisan ta tsawata ma hukumomin tsaron.

Patience Jonathan tace gwamnatin Buhari na cin zarafinta, ta kai wa majalisa kara

Patience Jonathan tace gwamnatin Buhari na cin zarafinta, ta kai wa majalisa kara

Dan majilasa mai wakiltan yankin Okrika na jihar rivers, Hon. Bright Tamuno ne ya gabatar da koken a gaban majallisan.

A yayin da take gabatar da koken, dan majallisan yayi kira da majalissar da ta sa baki a magannan, musamman idan an duba irin aiki da sadaukar da kai da mai gidan ta tsohon shugaba Jonathan yayi.

KUMA KU KARANTA: Baza mu iya dena karaban cin hanci ba - Yan sandan Anambra

Kamar yadda ya bayyana, yace babu wata Uwargidan shugaban kasar Najeriya da ta sha tsangwama kamar Uwargida Patience.

A cikin takardar koken, Uwargida Patience tana zargin hukumar EFCC da NDLEA da wasu hukomomin gwamnatin da musguna mata.

Kakakin majillisar, Mr Yakubu Dogara ya mika takardan koken ga kwamitin sauraran karar jama’a domin ta duba matsalar.

Patience Jonathan din dai ta taba shigar da kara makamancin haka a majallisar a watan disamba na shekara 2016.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel