Siyasa: Fiye da matasa 100 suka yi sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kogi

Siyasa: Fiye da matasa 100 suka yi sheka daga APC zuwa PDP a jihar Kogi

- Wasu kungiyar matasan jihar Kogi sun yi sheka daga APC zuwa PDP

- Shugaban kungiyar matasan ya ce rashin jika alkawuran gwamnatin jam’iyyar APC a jihar yasa su yin sheka

- Shugaban jam’iyyar PDP ya yi alkawarin cewa jam’iyyar za ta musu adalci

Jam’iyyar mai mulki ta kasa APC a Jihar Kogi ta samu koma-baya yayin da wasu matasan jihar suka yi m’iyyar zuwa jam’iyyar adawa PDP a karamar hukumar Ofu da ke jihar.

Da yake jawabi a madadin matasan a Agojoeju, mazabar Iboko / Efakwu da ke karamar hukumar Ofu, shugaban kungiyar matasan, Marvis ya dangana shawarar sheka zuwa jam'iyyar PDP a matsayin rashin jika alkawuran gwamnatin jam’iyyar APC a jihar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, a lokacin da ake ma kungiyar matasan lale maraba wanda aka gudanar a ofishin jam'iyyar PDP a mazabar Agojoeju Iboko / Efakwu, shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar, Hon Wajah Idris Attabo ya bayyana cewa ficewar matasan zai kawo karshen jam'iyyar APC a mazabar da kuma karamar hukumar baki daya.

KU KARANTA: Matsin tattalin arziki rahama ne ga Najeriya – Oyegun

Wajah ya yi alkawarin adalci ga kungiyar matasan mazabar don ci gaban jam’iyyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel