LABARI DA DUMI-DUMI: Babbar kotun Abuja ta dakatar da yi ma Melaye kiranye

LABARI DA DUMI-DUMI: Babbar kotun Abuja ta dakatar da yi ma Melaye kiranye

- Babbar kotun Najeriya da ke Abuja ta dakatar da INEC daga kiranyen sanata Melaye

- Sanata Melaye ya mika godiyarsa ga Yesu kan hukuncin kotun a shafinsa na Twitter

- Melaye ya kalubalanci yunkurin yi masa kiranye a babbar kotu da ke abuja

Babbar kotun Najeriya da ke birnin tarayyar Abuja ta dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) daga yi ma sanata Melaye mai wakiltar mazabar jihar Kogi ta yamma kiranye daga majalisar dattijai.

NAIJ.com ta ruwaito cewa babbar kotun ta yanke wannan hukunci ne yau Alhamis, 6 ga watan Yuli a Abuja.

Sanata Melaye ya wallafa a shafinsa ta Twitter cewa: "Na gode yesu, kotu ta dakatar da yukurin kiranyen karya. Yahaya Bello ne mai hasara”.

LABARI DA DUMI-DUMI: Babbar kotun Abuja ta dakatar da yi ma Melaye kiranye

Sanata Dino Melaye mai wakiltar mazabar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattijai Source: @NGRSenate

A farkon makon nan ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta saki lokacin da za ta fara yi ma sanatan kiranye daga majalisar dattijai.

KU KARANTA: Kiranye: Idan Sanata Melaye bai gamsu da aikin mu ba,ya tafi kotu-INEC

Sanata Melaye kuma ya kai karar hukumar a babbar kotun tarayya da ke Abuja inda yake kalubalantar yunkurin yi masa kiranye.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel