Shin akwai hukuncin shari'a a kan Sanata Bukar Abba da ya amsa cewa yana hulda da 'yan mata?

Shin akwai hukuncin shari'a a kan Sanata Bukar Abba da ya amsa cewa yana hulda da 'yan mata?

- Bidiyo mai badakala dai yayi ta yawo a yanar gizo inda aka ga sanata daga Yobe tumbur

- Sanatan ya ce ba ruwan jama'a da sabgarsa

- A shekarar 2000 dai shi gwamnan ya kaddamar da shari'ar Islama

Jaridar Sahara Reporters, a makon da ya gabata dai ta itar da wani faifan bidiyo da ya nuna Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Yobe, tumbur da 'yan-mata a wani kazamin daki wanda ke nuna kamar sun gama shakatawa ne.

A hira da aka yi dashi a BBC Hausa kuma, ya amsa cewa shi ne a wannan bidiyo, kuma ya zargi 'yan siyasa da neman yada wannan zance kan bata masa suna, inda yace ya barsu da Allah.

Shin akwai hukuncin shari'a a kan Sanata Bukar Abba da ya amsa cewa yana hulda da 'yan mata?

Shin akwai hukuncin shari'a a kan Sanata Bukar Abba da ya amsa cewa yana hulda da 'yan mata?

To sai dai, Sanata Bukar Abba Ibrahim da kansa, shekarun baya, ya rattaba hannu kan shari'ar Islama tayi aiki a jiharsa, wanda kuma ta haramta zina, da ma jefewa ga wanda hujja ta tabbata a kansu.

A irin wannan yanayi dai, inda ake shari'ar da gaske, idan duk hujjoji da shaidu suka cika, za'a jawo Sanatan ne, a kai shi daji a jefe har sai ya mutu, amma sai ga sanatan yace wannan abu harkarsa ce tasa, ba ruwan kowa a ciki.

KU KARANTA KUMA: Yan sandanda suka ce baza su iya dena karbar cin hanci ba

Idan akwai wani malami, wanda fatawarsa take da karfi, wanda kuma hurumin shari'ar jihar Yobe ta tabbata a hannunsa, yana da damar kirawo, kama da gurfanar da Sanatan gaban sharia domin a tantance gaskiyar lamarin. Idan aka yi hakan, shine an cika shari'a.

A yanzu dai, ga dukkan alamu, shari'ar da aka ce ana aiki da ita a wasu jihohin arewacin Najeriya ta tabbata ta siyasa ce kawai, kuma talaka ne kawai ake yi wa ita.

Wannan zai iya zama gaskiya, duba da yadda a shekarun mulkin wadannan mutane, aka kamo wata mata bazawara mai ciki Amina Lawal da wata Safiya Hussaini, aka yi ta kokarin yanke musu hukuncin jefewa, wai don angansu da ciki, ba kuma a taba jin an nemo wanda yayi cikin an hada dashi a hukuncin ba.

A jihar zamfara ma, an sami damar yanke wa wani barawon shanu hannu, kan satar shanu, kamar yadda shari'a ta tanada, amma a wancan lokacin ba'a ji irin su Sanata Bukar Abba sunce a kyale wannan mutane ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel