Hukumar Zabe: INEC ta tabbatar da karin cibiyoyin rajistar 6 a Jigawa

Hukumar Zabe: INEC ta tabbatar da karin cibiyoyin rajistar 6 a Jigawa

- INEC ta ta kafa karin cibiyoyin ‘rajistar masu jefa kuri’a guda 6 a wasu kananan hukumomin jihar

- Kananan hukumomin da aka yi karin sun hada da Dutse, Babura, Gwaram, Kafin Hausa, Suletankarkar da Guri

- Karin cibiyoyin ta biyo bayan jerin koke daga wasu mazaunar kananan hukumomin jihar game da nesan wuraren da ake rajistar

Hukumar zabe mai zaman kansa ta kasa (INEC) a Jihar Jigawa ta ce ta kafa karin cibiyoyin ‘rajistar masu jefa kuri’a guda 6.

Sakataren gudanarwa na hukumar a jihar, Malam Adamu Haladu, ya bayyana haka yayin da yake magana a wani taron da hukumar ta shirya a Dutse babban birnin jihar JIgawa a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli.

Haladu ya ce a kafa karin cibiyoyin shida 6 ne a wasu kananan hukumomi na jihar.

Hukumar Zabe: INEC ta tabbatar da karin cibiyoyin rajistar 6 a Jigawa

Katin jefa kuri'a

NAIJ.com ta ruwaito ceawa, sakataren ya ce ƙarin cibiyoyin sun hada da kananan hukumomin Dutse, Babura, Gwaram, Kafin Hausa, Suletankarkar da Guri.

KU KARANTA: Ni ban baiwa Majalisar Kano cin hancin miliyan N100 ba - Inji Dangote

Ya ce: “Mun kafa karin cibiyoyin ne bayan da muka samu jerin koke daga wasu mazaunar kananan hukumomin jihar game da nesan wuraren da ake rajistar”.

Haladu ya kuma shawarci 'yan siyasa da su wayar da kan mutanen mazabarsu kan bukatar yin rajistar da kuma samun katin zabe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel