Gwamna Ganduje ya canza ma jami’ar Kano suna zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule

Gwamna Ganduje ya canza ma jami’ar Kano suna zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule

- Gwamnatin Kano ta sauya sunan jami'ar North West

- Gwmanatin ta sauya sunan ne suna jami'ar Yusuf Maitama Sule

A ranar Alhamis 6 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta zartar da hukuncin sauya sunan sabuwar jami’ar North West dake Kano zuwa jami’ar Yusuf Maitama Sule.

Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya bayyana gwamnatin ta dauki wannan mataki ne sakamakon gudunmuwar da marigayi Danmasanin Kano ya bayar ga jihar Kano, Arewa da Najeriya gaba daya.

KU KARANTA: Fadar shugaban ƙasa tayi hannun riga da kalaman muƙaddashin shugaban ƙasa Osinbajo

An dauki wannan mataki ne biyo bayan wani zaman gaggawa da majalisar zartarwar jihar Kano ta yi a fadar gwamnatin jihar a daren Laraba 5 ga watan Yuli, kamar yadda mashwarcin gwamna Ganduje akan watsa labaru Salihu Tanko Yakasai ya bayyana.

Gwamna Ganduje ya canza ma jami’ar Kano suna zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule

Tsohuwar jami'ar North West

Haka zalika majalisar ta amince da sauya sunan titin zuwa gidan Maitama Sule daga titin Dawaki zuwa titin Yusuf Maitama Sule, yayin da shi kuma tsohon titin Yusuf Maitama Sule an canza masa suna zuwa titin Jafaru Dan Mallam.

Sanarwar ta bayyana cewar a shirye gwamna Ganduje yake ya karrama yayan jihar Kano wadanda suka bada gagarumar gudunmuwa ga jihar.

Gwamna Ganduje ya canza ma jami’ar Kano suna zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule

Jami'ar Yusuf Maitama Sule

Sai dai NAIJ.com ta ruwaito an samu bayyananr ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin al’ummar jihar, inda hatta wasu dalibai sun soki wannan mataki, yayin wasu kuma sukayi san barka da shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga Buhari ga Osinbajo, wa zaka zaba?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)

Bambarakwai: Uwargida zata biya ma Maigida sadaki don ya kara aure (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel