Ku rabu da AbdulAziz Yari fa – sakon Kungiyar Gwamnoni ga hukumar EFCC

Ku rabu da AbdulAziz Yari fa – sakon Kungiyar Gwamnoni ga hukumar EFCC

- Kungiyar gwamnonin rukunin shiyar Arewacin kasar ta yi kira ga hukumar dake yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa kan shugaban kungiyar

- Su nemi hukumar ta rabu da shi domin ya mayar da hankalinsa ga shugabancin kungiyar da kuma jiharsa

- Wannan ya biyo bayan zargi da akayi masa da mallakar wani otel na miliyoyin daloli a jihar Lagas

Kungiyar gwamnonin rukunin shiyar Arewacin kasar ta yi kira ga hukumar dake yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC kan ta daina matsa ma shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari da ta keyi

Wannan ya biyo bayan wani rahoto da wani gidan jarida ya kawo kan zargin cewa gwamnan na gina wani katafaren masaukin baki a jihar Legas da akalla ya kai kimanin dala miliyan uku.

Mai Magana da yawun kungiyar Abdulrazak Barkindo ya ce gwamnonin sun ce hukumar ta daga ma gwamna AbdulAziz kafa saboda ya samu damar mayar da hankalinsa da tunaninsa wajen jagorancin kungiyar da kuma jiharsa.

Ku rabu da AbdulAziz Yari fa – sakon Kungiyar Gwamnoni ga hukumar EFCC

Ku rabu da AbdulAziz Yari fa sakon Kungiyar Gwamnoni ga hukumar EFCC

“Abdul Aziz yari ya jaddada cewa bai mallaki wani fili ko wata Otel da ya ke ginawa a jihar Lagas ba.”

KU KARANTA KUMA: An kashe mutun daya yayinda dan majalisa ya tsallake rijiya da baya

Sun yi kira ga hukumar EFCC din da su mai da hankalinsu wajen kamo masu laifi ba wadanda ba su da laifin komai ba face kage.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel