Matsin tattalin arziki rahama ne ga Najeriya – Oyegun

Matsin tattalin arziki rahama ne ga Najeriya – Oyegun

- Oyegun ya ce matsin tattalin arziki rahama ce ga Najeriya

- Ya bayyana hakan a taron da ake gudanarwa duk shekara a kan noma

- Ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta mayar da hankali gurin bunkasa bangaren noma tare da janye hankalin jamaá daga man fetur

Babban jigo kuma shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress ta kasa, John Odigie-Oyegun ya sanar da cewa matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta a yanzu Rahama ce ga kasar a fakaice.

Shugaban jaamíyyar ta APC ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 4 ga watan Yuli a wajen taron shekara-shekara akan noma wanda aka yi a jami’ar Benin.

Oyegun ya ce ba don matsin tattalin arzikin ba, babu wanda zai yi tunanin Najeriya za ta iya ciyar da kanta ko bazata iya ba, wanda hakan Rahama ce ga Najeriya a fakaice.

Matsin tattalin arziki rahama ne ga Najeriya – Oyegun

Matsin tattalin arziki rahama ne ga Najeriya inji Oyegun

Ya kara da cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta mayar da hankali gurin bunkasa bangaren noma tare da janye hankalin jamaá daga man fetur.

KU KARANTA KUMA: EFCC tayi yunkuri a kan ‘yan majalisa, tana yunkurin kama wasu Sanatoci

Oyegun ya bayar da misali da kasar Amurka, inda ya ce gwamnati na biyan manoma domin su noma har kayan abincin da ba su da bukatar su.

Ya ce mun kai wannan matsayin saboda farashin man fetur a kullum rikitowa yake.

A cewar shi “Ya zama dole mu koma ga noma. Mun dade muna shiririta ba tare da wata alkibla ba”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel