'Magabtan Najeriya ne ke son Bayafara, sake tsarin Najeriya kuma yaudarar siyasa ce'

'Magabtan Najeriya ne ke son Bayafara, sake tsarin Najeriya kuma yaudarar siyasa ce'

- Magabtan Najeriya lallai makiyan Kasar ne

- Sake tsarin Najeriya Yaudarar siyasa ce

- Mulkin Najeriya a hannun Buhari shi zai dawo da martabarta

Gwamnan Jahar Kogi Yahaya Bello ya bayyana magabtan Najeriya lallai makiyan Kasar ne. Ya kuma yi kira da ‘yan Najeriiya da suyi watsi da sake tsarin Kasa, domin sake tsarin Kasar nan yaudarar siyasa ce.

A cewar yahaya Bello ‘'mulkin Najeriya a hannun Shugaba Muhammadu Buhari shine hanya mafi dai-dai domin shine zai dawo da martabar Kasar nan.’

'Magabtan Najeriya ne ke son Bayafara, sake tsarin Najeriya kuma yaudarar siyasa ce'

'Magabtan Najeriya ne ke son Bayafara, sake tsarin Najeriya kuma yaudarar siyasa ce'

Ya kuma bayyana cewa kowace Kasa da irin nata kalubalen da take fuskantar, amma tana kokarin taga ta shawo kan matsalolinta, ba tare da la’akari da banbancin addini, siyasa ko al’ada ba.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sandan da suka ce baza su iya dena karbar na goro ba

Gwamna Bello yayi kira da ‘yan Najeriya da su zamo masu kishin kasar su. Su zamo masu neman zaman lafiya da bin dokokin da Gwamnati ta shimfida domin kasar Najeriya kasa ce mai albarka. Yana kara rokon yan Najeriya da su bawa Gwamnatin tarayya goyon bayan ganin ta gyara matsalolin da suka faru a mulkin baya.

Tun bayan hawan Gwamnan mulki, Gwamnatinsa ta dau matakai masu karfi don ganin ta inganta kayayyakin more rayuwa irin su tituna, samar da ruwa, da ingantaccen asibitoci ga mutanen Jahaf ta.

Tayi kokarin biyan ma’aikata albashin su, da duk bashin da suke bi. Haka suma 'yan fensho bata bar su a baya ba wajen biyan su basussukan su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel