Ayyuka 1,170 da suka haddasa rigima tsakanin Majalisa da Fashola

Ayyuka 1,170 da suka haddasa rigima tsakanin Majalisa da Fashola

- An gano arigizo da yawa da majalisar tayi kan kasafin kudin bana a ayyuka

- Majalisar kuma ta zaftare kudaden muhimman ayyuka da yawa

- Ana cacar kalamai tsakanin Ministan ayyuka da Majalisa

A kasafin kudin bana dai, majalisar Tarayya ta jefa wasu karin ayyuka dubu daya bayan wadanda ma'aikatar aiki da makamashi ta tura. An sako karin ne a kan kudaden da aka kasafta don manyan ayyukan tarayya.

Wannan katsalandan ya bata wa Minista Fashola rai, inda ya jefa wa Majalisar kalamai zafafa, su kuma suka mayar masa da idan ya gaza, ko ya gaji, ya ajje aikin ya tafi gida.

Ayyuka 1,170 da suka haddasa rigima tsakanin Majalisa da Fashola

Ayyuka 1,170 da suka haddasa rigima tsakanin Majalisa da Fashola

A cikin aringizon dai, sun kara aiyuka 1170, nayan wadanda aka rattaba za'ayi a ka'idance, 308 daga cikin wadannan karin ayyuka an tsomo su ne a aikin FERMA na gyaran tituna, 456 kuma a aikin kai wuta karkara da kauyuka.

KU KARANTA KUMA: Baza mu iya dena karbar N20 a tituna ba, 'yan-sanda

An kuma harba kudaden aikin ma'aikatar da biliyoyin kudi, daga naira biliyan 564, zuwa naira biliyan 586.

A gefe daya kuma, muhimman ayyuka kamar fadada hanyar Abuja-Lokoja mai yawan kashe mutane, an gutsure kudinta daga biliyan 9 zuwa biliyan 7.

An dai gano irin wannan a ko'ina a cikin wannan kasain kudin ma'aikatar na bana, kuma har Shugaba Osinbajo ya rigaya ya saka hannu, wanda hakan na nuin kare-karen sun shiga, ya rage na ministan ko ya nemo kudin yayi musu wadannan ayyuka, ko ya gaza.

Ministan dai bai ji dadin wannan aringizo da katsalandan kan ayyukansa ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel