Manchester United ta amince ta sayi Romelu Lukaku kan fan miliyan 75

Manchester United ta amince ta sayi Romelu Lukaku kan fan miliyan 75

- An rahoto cewa Manchester United ta yarda da siyan dan wasan gaba na Everton

- Jarumin kwallon kafar da ya fito daga kasar Belgium na da halaka da wani yunkuri da Chelsea

- Tawagar ta Jose Mourinho na fatan kammala cinikin dan wasan kafin kungiyar ta tafi Amurka domin atisayi ranar Lahadi

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yarda da siyan Romelu Lukaku, dan wasan gaba na Everton kan kudi fan miliyan 75.

Jarumin dan kwallon kafar mai shekara 24 na kasar Belgium ya zira kwallo 25 a gasar Firimiyar da aka kakkare.

Manchester United ta amince ta sayi Romelu Lukaku kan fan miliyan 75

Manchester United ta amince ta sayi Romelu Lukaku kan fan miliyan 75

Manchester United, wacce ta jima tana harin Lukaku, ba za ta ci gaba da neman dan wasan Real Madrid Albaro Morata ba.

KU KARANTA KUMA: An kashe mutun daya yayinda dan majalisa ua tsallake rijiya da baya

Tawagar Jose Mourinho na fatan kammala cinikin dan wasan kafin kungiyar ta tafi Amurka domin atisayi ranar Lahadi.

Lukaku na daga cikin rukunin 'yan wasan da Mourinho ya bai wa mukami na mataimakin shugaban kungiyar, Ed Woodward kafin karshen kakar wasan bara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel