An kashe mutun daya yayinda dan majalisa ya tsallake rijiya da baya

An kashe mutun daya yayinda dan majalisa ya tsallake rijiya da baya

- Mista Oladipupo Adebutu ya tsallake rijiya da baya

- Dan majalisan ya tsallake rijiya da baya ne a Ota, karamar hukumar Ado-Odo/Ota dake jihar Ogun a daren ranar Laraba

Dan majalisar cdake wakiltan mazabar Ikene/Shagamu/Remo North, Mista Oladipupo Adebutu ya tsallake rijiya da baya a Ota, karamar hukumar Ado-Odo/Ota dake jihar Ogun a daren ranar Laraba.

A cewar rahotanni, wasu da ake zargin yan iskan siyasa ne sun bude wuta ga ayarin motocin sa da misalin karfe 7:00 na yamma inda suka kashe daya daga cikin magoya bayansa a yankin Oke-Ide na garin.

An rahoto cewa dan majalisar na a hanyarsa ta dawowa daga wani taro na jam’iyyar PDP a Aiyetoro, hedkwatar karamar hukumar Yewa North.

KU KARANTA KUMA: EFCC tayi yunkuri a kan ‘yan majalisa, tana yunkurin kama wasu Sanatoci

An rahoto cewa ya yada zango ne a Ota don kai wani ziyara ga wasu mambobin jam’iyyar da aka kama lokacin da aka kai masa hari.

A cewar idon shaida, an harbe wani dan fadar dan majalisar da ba a bayyana sunansa ba, sannan kuma yam utu a take a gurin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel