YANZU-YANZU: Kotu tayi watsi da karar da El-Zakzaky ya shigar kotu kan hukumar sojin Najeriya

YANZU-YANZU: Kotu tayi watsi da karar da El-Zakzaky ya shigar kotu kan hukumar sojin Najeriya

-Kotu tayi watsi da bukatan yan kungiyar Shi'a kan laftanan janar Buratai

Wata babban kotun Najeriya da ke zaune a Kaduna ta yanke cewa karar da shugaban kungiyar mabiya Shi’a, Ibrahim Zakzaky, ya shigar kan hukumar sojin Najeriya, shugaban hukumar sojin kasan da kuma wasu 2 akan take hakkin dan Adam cin mutunci ne ga ka’idojin kotu.

Amma lauyan El Zakzaky, Mr. Festus Okoye, yace sam ba haka bane, abinda aka bukata a babban kotun tarayya da ke Kaduna ya banbanta da wanda aka shigar a babban kotun Abuja karkashin alkali Jastis Gabriel Kolawole.

YANZU-YANZU: Kotu tayi watsi da karar da El-Zakzaky ya shigar kotu kan hukumar sojin Najeriya

YANZU-YANZU: Kotu tayi watsi da karar da El-Zakzaky ya shigar kotu kan hukumar sojin Najeriya

Yace lauyoyinsa zasu natsu su lura da zancen kafin daukan matakin daukaka kara ko a’a.

El-Zakzaky ya bukaci hukumar sojin ta biyashi kudi N2bn akan lalata da cin mutuncin da aka masa.

KU KARANTA: Ba zamu iya daina karban cin hanci ba - Yan sanda

A ranan 12 ga watan Disamba 2015, hukumar sojin Najeriya ta samu takaddama da yan kungiyar Shi'a a garin Zariya yayinda yan kungiyar suka hana babban hafsan sojin Najeriya, Tukumar Buratai, wucewa.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/?business_id=663027310546163#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel