Za a samar wa matasan Najeriya 6,900 ayyukan yi

Za a samar wa matasan Najeriya 6,900 ayyukan yi

- Shirin Fadama III zata samar wa matasan wasu jihohi 23 ayyukan yi

- Malam Bashir Dayyabu ya ce ba sanar da suna jihohi 23 da zasu amfana da shirin ba

- Jihohin Anambra, Nejar, Kogi, Kano, Enugu da kuma Legas suka fi more shirin na Fadama III

Shirin karin tallafin kudi ga Fadama III wato FADAMA III Additional Financing (AF) ta ce za ta horar da matasa 6, 900 a fanin aikin noma da kuma kasuwanci a jihohi 23 a fadin kasar.

Jami’in sadarwa na AF ta kasa, Malam Bashir Dayyabu ya bayyana haka a Minna babban birnin jihar Neja a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli a lokacin wata taron FADAMA III.

Dayyabu wanda bai ba da suna jihohi 23 da zasu amfana da shirin ba, ya ce bayan horor na mako biyu da za a yiwa matasan, za a sama masu tallafin kudi wanda zasu iya fara aikin gona ko kasuwanci.

Za a samar ma matasan Najeriya 6,900 ayyukan yi

Shirin FADAMA III Additional Financing (AF) source: fadamaaf.net

Dayyabu ya ce: '' Mun fara tantance matasa 6, 900 da zasu amfana a cikin wannan shirin na aikin noma a jihohi 23 a fadin kasar”.

Ya ce shirin da aka sani da '' Fadama Guys '' na wani bangare ne na kokarin da gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma Bankin Duniya ke yi don samar da ayyukan yi ga matasa da kuma inganta aikin noma.

KU KARANTA: Jirage 3 sun isa tashoshin jiragen ruwa da man fetur, da wasu kayayyakin abinci

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewa jihohi 6 da suka fi more shirin Fadama III sun hada da Anambra, Nejar, Kogi, Kano, Enugu da kuma Legas.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel