Karya ne! Gwamnatin jihar Kano bata canza sunan jami'ar North West zuwa Dan Masani ba

Karya ne! Gwamnatin jihar Kano bata canza sunan jami'ar North West zuwa Dan Masani ba

- Gwamnatin jihar Kano, ta karyata jita-jita da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani cewa ta canja wa jami'ar NorthWest dake Kano suna zuwa na marigamayi Matama Sule.

- Da ya ke maida martani kan wannan jita-jitar, babban jami'in watsa labarai na gwamnan jihar Kano Abdullahi Tanko Yakasai, ya ce gwamnatin Kano ba ta canjawa jami'ar suna da sunan kowa ba.

NAIJ.com ta samu labarin cewa dai kamar yadda jaridar Daily Nigeriya ta ruwaito da yamman nan, Salihu Yakasai ya cigaba da cewa, jita-jita ce kawai, domin yau ne daman za a yi zaman majalisar zartarwa, sai aka daga zuwa gobe Alhamis 6 ga wannan wata domin mai girma gwamna Abdullahi Ganduje yana wurin karbar gaisuwar rashin Dan Masanin Kano.

Karya ne! Gwamnatin jihar Kano bata canza sunan jami'ar North West zuwa Dan Masani ba

Karya ne! Gwamnatin jihar Kano bata canza sunan jami'ar North West zuwa Dan Masani ba

Jami'in ya kara da cewa, sai majalisar zartarwa ta zauna gobe, kafin a ga ko akwai yiwuwar hakan, domin karrama marigayin.

Sugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola saraki, ya shawarci gwamnatin tarayya da na jihar Kano da ta karrama marigayi Dan Masanin Kano ko dan kara tunawa da shi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel