Fr. Mbaka ya saki bam a kan lafiyar Buhari, ya ce ya ji kuka daga Aso rock

Fr. Mbaka ya saki bam a kan lafiyar Buhari, ya ce ya ji kuka daga Aso rock

- Fada Ejika Mbaka ya karya shiru a kan lafiyar Buhari

- Babban fasto din ya ce anyi masa wahayi cewa akwai kuka kamar ruwan sama daga Aso rock

- Ya bayyana cewa akwai lokacin da ya fada ma Buhari cewa mutane na shirin kashe shi amma babu wanda ya saurare shi

Babban fasto dinnan mai da’awa, Fada Ejike Mbaka ya sake aman wuta a kan lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mbaka, wanda yayi magana a lokacin wani shirin mako mai taken ‘E No Dey Again’ wanda aka gudanar a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, ya ce ya ji wani kuka kamar zubar ruwan sama daga Aso rock.

NAIJ.com ta tattaro cewa malamin ya ce anyi mai wahayi kan ya yi gaggawan zuwa Aso Rock amma da ya kai chan, babu wanda ya shirya kai shi inda Buhari yake a Landan.

Fr. Mbaka ya saki bam a kan lafiyar Buhari, ya ce ya ji kuka daga Aso rock

Fr. Mbaka ya saki bam a kan lafiyar Buhari, ya ce ya ji kuka daga Aso rock

Malamin ya ce ya samu wahayi inda ya halarci wani taro a Aso Rock, wanda Ibrahim Babangida ma ya halarta.

KU KARANTA KUMA: Najeriya zata fara fita da gasasshiyar gyadar kashu zuwa kasar Japan – Audu Ogbeh

“Na tambayi IBB wani tambaya game da Buhari amma sai ya ce mun na manta kawai. Akwai kuka kamar ruwan sama a Aso Rock da arewa. A duniyar ruhanai, tutar Najeriya na kuna. Cikin dan kankanin lokaci abun da ake boyewa zai bayyana,” cewar sa.

Ya kuma tuna cewa akwai lokacin da ya fada ma Buhari cewa mutane na shirin kashe shi amma babu wanda ya saurare shi.

Ya kuma bayyana cewa kafin Buhari ya yi tafiya, ya samu wahayi inda Allah ya fada masa ya je ya yi masa addu’a amma wadannan mutane na Aso Rock basu bar shi ya shiga ba.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya kuma kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus domin amfanin kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel