To fa! Majalisar dattijai zata far bincikar ma'aikatar Hadiza Bala Usman kan badakalar $3biliyan

To fa! Majalisar dattijai zata far bincikar ma'aikatar Hadiza Bala Usman kan badakalar $3biliyan

- Majalisar dattijai ta sha alwashin bincikar hukumar NPA

- Majalisa tace tayi aringizo wajen bada kwantaragi

- Majalisa zata bayar da rahoton ta cikin sati daya

Majalisar dattijan Najeriya karkashin jagorancin shugabanta Bukola Saraki a jiya ta dorawa kwamitin ta mai kula da harkokin ruwa da ya binciki hukumar nan ta mai kula da tashoshin ruwa watau Nigerian Port Authority (NPA) a turance.

Majalisar dai tace a binciki hukumar ne saboda wasu yan matsaloli da kuma rashin yin dai-dai a wadansu kwantaragin da ta bayar na gyaran wasu tashoshi a Legas da kuma jihar Kalaba.

To fa! Majalisar dattijai zata far bincikar ma'aikatar Hadiza Bala Usman kan badakalar $3biliyan

To fa! Majalisar dattijai zata far bincikar ma'aikatar Hadiza Bala Usman kan badakalar $3biliyan

NAIJ.com ta samu labarin cewa kudaden da aka kashe wajen wannan kwantaragin dai sun tasar wa zunzurutun kudin har $3biliyan.

Kwamitin dai Sanata Ahmad Yariman Bakura ne ke jagorantar sa kuma zasu bada rahoton su cikin sati daya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel