Yesu Almasihu ne yasa na maida albashin da aka bani na N60,000 bayan na bar aikin N-Power - Joshua

Yesu Almasihu ne yasa na maida albashin da aka bani na N60,000 bayan na bar aikin N-Power - Joshua

- Mr. Daniel Joshua dai dan jihar Taraba ne

- Mr. Daniel Joshua ya mayar da albashin wata 2 da aka bashi na N-power bayan ya samu aiki

- Mr. Daniel Joshua ya ce Yesu Almasihu ne ya sa shi

Wani matashi mai shekaru 31 daga jihar Taraba mai suna Daniel Joshua ya ba matasa da dama mamaki yayin da ya mayar da albashin sa na wata 2 da aka bashi a cikin shirin nan na N-power.

Matashin dai ya bayyana cewa bayan ya samu aiki a babban bankin Najeriya watau CBN amma kuma N-power ta sake biyan sa sai ya yanke shawarar ya maida masu kudin su.

Yesu Almasihu ne yasa na maida albashin da aka bani na N60,000 bayan na bar aikin N-Power - Joshua

Yesu Almasihu ne yasa na maida albashin da aka bani na N60,000 bayan na bar aikin N-Power - Joshua

NAIJ.com ta samu labarin cewa matashin mai suna Daniel Joshua yace tsananin imanin sa da Yesu Almasihu ne ya sa shi ya maida wadan nan kudin bayan ya karbe su.

A kwanan baya ne dai mukadashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bukaci yan Najeriya da su yi koyi da wannan matashi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel