Kunji yaushe Lionel Messi zai bar kungiyar Barcelona?

Kunji yaushe Lionel Messi zai bar kungiyar Barcelona?

- Lionel Messi ya sa hannu a kwantaragin sa da Barcelona

- Messi zai tsaya kungiyar har nan da 2021

- Messi dai yanzu shekarun sa 30 a duniya

Shararren dan wasan nan na gaba na kungiyar Barcelona watau Lionel Messi ya amince da ya ci gaba da zama a kungiyar tasa har nan da shekaru hudu masu zuwa watau shekara ta 2021.

Yanzu haka dai dan wasan shekarun sa 30 kuma ya fara buga wasa a kungiyar ta Barcelona tun yana da shekaru 13 kacal a duniya.

Kunji yaushe Lionel Messi zai bar kungiyar Barcelona?

Kunji yaushe Lionel Messi zai bar kungiyar Barcelona?

NAIJ.com ta samu labarin cewa Kulob din da ke buga wasan La Liga ya ce, "Kulob din nan na matukar farin ciki da sabunta kwantaragi da Messi zai yi, kasancewarsa gwanin dan wasa na tarihi."

Ya zuwa yanzu dai dan kungiyar ta Barcelona ya zura kwallayen da suka zarce 500 a cikin wasanni 583 tun daga shekara ta 2004 da ya fara.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel