Sojoji sun yi ma Boko Haram aman wuta a wani yankin dajin Sambisa

Sojoji sun yi ma Boko Haram aman wuta a wani yankin dajin Sambisa

- Sojojin rundunar sama sun kai harin bamabamai akan Boko Haram

- Harin ya faru ne a sansanin yan Boko Haram dake kauyen Alagarno, dajin sambisa

Rundunar mayakan Sojin sama sun yi ruwan bamabamai a wata mafakar mayakan Boko Haram dake wani sashi na dajin Sambisa a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli.

Rundunar ta bayyana cewa yayin wani sintiri a sararin samaniya da take yi a dajin Sambisa, ta lura wasu mayakan Boko Haram na taruwa a wasu gine gine a sansanin Alagarno.

KU KARANTA: Kiranye: Idan Sanata Melaye bai gamsu da aikin mu ba,ya tafi kotu-INEC

Rundunar tace ta gano mafakar ne sanadiyyar na’urar samar da wutan lantarki da dama wanda mayakan na Boko Haram ke amfani dasu a dajin.

Sojoji sun yi ma Boko Haram aman wuta a wani yankin dajin Sambisa

Harin

“A ranar 3 ga watan Yuli ne muka aika da jiragen yaki guda 3 inda suka dinga luguden wuta akan mafakar yan ta’addan, daga bisani na’urar mu ta daukon hotuna ta bayyana mun lalata kafatanin gidan gaba daya.

“Sa’annan mun samu nasarar jefa bom kan wata motar yan ta’addan da tayi yunkurin tserewa daga wajen.” Kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ga dai bidiyon nan kamar yadda NAIJ.com ta dauko shi daga shafin rediyon jami’an Soji dake kan Facebook.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sabbin sojojin rundunar sojan sama matuka jirgin yaki, kalle su:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel