Mukaddashin shugaban ƙasa Osinbajo ya gasa ma Saraki magana - KARANTA

Mukaddashin shugaban ƙasa Osinbajo ya gasa ma Saraki magana - KARANTA

- Bukatar nada Shugaban majalisar dattawa Sanata Saraki mukaddashin shugaban kasa ta bar baya da kura

- Osinbajo ya aika ma majalisar sako mai cike da maganganu

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa duk masu kaunar ganin sun dare kujerarsa ta shugabancin Najeriya na riko toh su sauya tunani.

Osinbajo yace “Kamata yayi masu bukatar ganin sun zama mukkadashin shugaban kasa su koma su fara fahimtar yadda sa ido a ayyukan gwamnati tukunna, da haka ne zasu gudanar da ayyukan da aka zabe su su gudanar.”

KU KARANTA: An tsinci wani jariri rufe a cikin kwali a Maƙabartar Kaduna (HOTUNA)

Wadannan kalamai sun biyo bayan wata bukata da Sanata Kabiru Marafa ya gabatar a zaman majalisar dattawa ne inda ya bukaci tunda shugaban kasa Muhammadu Buhari yana birnin Landan, kuma mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya tafi taro a kasar Ethiopia, to kamata yayi a nada shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki mukamin mukaddashin shugaban kasar Najeriya.

Mukaddashin shugaban ƙasa Osinbajo ya gasa ma Saraki magana - KARANTA

Mukaddashin shugaban ƙasa Osinbajo tare da Saraki da Dogara

Sai dai hakan bai yi ma Osinbajo dadi ba, inda ya kara da cewa “Don kuwa a yanzu babu abinda suke yi in banda cutar da yan Najeriya, da kuma cece kuce.

“Don haka, kowa ma ya sani, babu wani gurbin mayewa a fadar shugaban kasa, kowa ya tsaya yayi ma yan Najeriya aikin da aka zabe shi yayi.”

Sai dai dayake martani, NAIJ.com ta ruwaito Sanata Saraki yana musanta shinsjinar kujerar mukaddashin shugaban kasar, inda yace na zai taba raina mukaminsa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Buhari da Osinbajo wanene gwaninka, Kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel