Boko Haram: Fiye da 70 mayakan kungiyar Boko Haram sun mika wuya a Borno

Boko Haram: Fiye da 70 mayakan kungiyar Boko Haram sun mika wuya a Borno

- Akalla mayakan Boko Haram 70 suka mika wuya ga sojoji a Maiduguri

- Babban kwamandan na Operation Lafiya Dole ya ce maharan sun mika wuya ne da kansu

- Daya daga cikin maharan ya kira sauran ‘yan Boko Haram da su ajiye makamai, su rungumi zaman lafiya

Akalla mayakan Boko Haram 70 suka mika wuya ga sojojin Najeriya a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli a garin Maiduguri babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Manjo Janar Ibrahim Attahiru, babban kwamandan na Operation Lafiya Dole ne ya bayyana hakan yayin gabatar da mayakan ga manema labarai a garin Maiduguri.

Attahiru ya ce maharan sun mika wuya ne da kansu biyo bayan dabarun daban-daban na gwamnatin tarayya don kawo karshen ta’addanci a yakin arewa maso gabashin kasar.

Kwamandan ya ce: " Maharan 700 ko fiye da haka yanzu sun yi niyyar mika wuya ga sojoji”.

Daya daga cikin maharan ya kira saura mayakan Boko Haram da babban murya da su mika wuya.

Maharan ya ce: “Ina kira ga sauran yan Boko Haram su ajiye makamai, su rungumi zaman lafiya da kuma shiga cikin al'umma”.

KU KARANTA: Ta'addancin Boko Haram ya sake leka Diffa ta Nijar

NAIJ.com ta ruwaito cewa, a farkon makon nan babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya sanar da cewa fiye da 700 'yan kungiyar Boko Haram suka mika wuya ga sojojin na Operation Lafiya Dole da ke Borno.

Buratai ya ci gaba da cewa wasu maharan kungiyar da dama na shirin mika wuya ga sojoji.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel