Fadar shugaban ƙasa tayi hannun riga da kalaman muƙaddashin shugaban ƙasa Osinbajo

Fadar shugaban ƙasa tayi hannun riga da kalaman muƙaddashin shugaban ƙasa Osinbajo

Fadar shugaban kasa ta wanke kanta daga wasu kalamai da ake zargin mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya furta dangane da rashin tantance wasu jami’an gwamnati da aka nada, inda yace wasu mukamai basu bukatar tantancewar majalisar dattawa.

Ministan shari’a kuma lauyan gwamnati, Abubakar Malami tare sa babban mashawarcin shugaban kasa kan lamurran watsa labaru, Garba Shehu ne suka bayyana haka, inda suka ce majalisar zartarwa bata tattauna wannan batu ba.

KU KARANTA: An tsinci wani jariri rufe a cikin kwali a Maƙabartar Kaduna (HOTUNA)

Daily Trust ta ruwaito a ranar Laraba 5 ga watan Yuli ne majalisar Dattawa ta yanke hukuncin dakatar da tantance duk wani jami’in gwamnati da bangaren zartarwa ta aiko mata da sunansa domin nada shi mukami.

Fadar shugaban ƙasa tayi hannun riga da kalaman muƙaddashin shugaban ƙasa Osinbajo

Osinbajo, Malami da Garba

Majalisar dattawan da yanke wannan hukunci ne biyo bayan kin amincewa da sallamar shugaban hukumar EFCC da shugaban kasa Muhammadu Buhari yaki yayi ne, wanda tace bai dace ya cigaba da zama a mukamin ba.

Malami yace “Dangane da wadannan kalamai, majalisar zartarwa bata tattaunawa ba akan batun ko daukan matsaya ba dangane da batun. Don haka wannan ba ra’ayinta majalisar bane.” Kamar yadda majiyar NAIJ.com ta jiyo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Da Buhari da Osinbajo wa yafi iya mulki?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Legas a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel