Sheriff ya zargi tsofaffin ministocin gwamnatin PDP da satar kuɗin Al’umma

Sheriff ya zargi tsofaffin ministocin gwamnatin PDP da satar kuɗin Al’umma

- Shugaban jam'iyyar PDP ya kalubalanci ministocin PDP su bayyana tushen arzikinsu

- Sheriff ya zargi ministocin da mallakan makudan kudade

Shugaban jam’iyyar PDP, Sanata Ali Modu Sheriff ya kalubalanci tsoffin ministocin gwamnatin PDP data shude dasu bayyana ma yan Najeriya inda suka samu kudaden su.

Daily Trust ta ruwaito Sheriff na zargin tsoffin ministocin da mallakan makudan kudade na fitar hankali, wanda har ya kai matsayin da zasu iya siyan jam’iyyar gaba daya.

KU KARANTA: Dakarun Soji sun hallaka sojojin haya na Boko Haram a ƙauyen Gulumba (HOTUNA)

Wannan zargi na Sheriff ya biyo bayan wani taro daya gudana ne a ranar Litinin 2 ga watan Yuli, inda tsoffin ministocin PDP suka tabbatar da goyon bayansu ga Sanata Ahmad Makarfi, sa’annan suma sun zargi gwamnatin APC da rarraba kawunan yan Najeriya.

Sheriff ya zargi tsofaffin ministocin gwamnatin PDP da satar kuɗin Al’umma

Sheriff

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito mataimakin jam’iyyar PDP Dakta Cairo yana cewa “Ministocin nan suna makudan kudade wanda ba’a san inda suka samo kudaden ba, kuma su burinsu shine su siye jam’iyyar. Amma Sheriff yace ba zai yarda ya siyar da jam’iyyar ba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wacce kasa zaka koma idan an raba Najeriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel