Kiranye: Idan Sanata Melaye bai gamsu da aikin mu ba,ya tafi kotu-INEC

Kiranye: Idan Sanata Melaye bai gamsu da aikin mu ba,ya tafi kotu-INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta bayyana cewar babu wanda ya isa ya kawo mata tsaiko a aikin da take yin a bukatar yi ma Sanata Dino Melaye kiranye daga majalisar dattawa kamar yadda yan mazabarsa suka bukata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito mai magana da yawun shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmoud Yakub, Rotimi Oyekanmi yana bayyana haka a ranar Talata 4 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Kwaya ce: Ýan mata da matan Aure sun koma harkar shan ƙwaya da kayan maye – Inji NDLEA

Kaakakin yace son Melaye ya shigar da kara gaban kotu ba zai hana hukumar INEC gudanar da aikinta ba har sai Kotu ta bada umarnin a dakatar da aikin, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Kiranye: Idan Sanata Melaye bai gamsu da aikin mu ya tafi Kotu – INEC

Sanata Melaye

A ranar Litini 3 ga watan Yuli ne INEC ta fitar da jadawalin tantance kuri’un jama’an da suka nuna bukatar dawo da Melaye gida, inda ta sanya ranar 19 ga watan Agusta a matsayin ranar tantancewar.

Sai dai Kaakakin yace babu gudu babu ja da baya game da manufar INEC na yin aikinta ba tare da katsalandan ba, ko shiga sharo ba shanu, tun da dai suna bin tsarin aikin hukumar ne.

Kaakakin ya kara da cewa “Za’a fara tantace kuri’un ne a ranar 10 ga watan Yuli 2017, kuma zamu bi duk hanyoyi da suka dace wajen tantance kuri’un, amma idan masu kuri’un basu bayyana gaban mu ba, shikenan aiki ya tsaya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel