Ina da dukiya a Dubai kafin na zama hafsoshin soja – Inji Buratai

Ina da dukiya a Dubai kafin na zama hafsoshin soja – Inji Buratai

- Babban hafsan sojan Najeriya ya amince cewa yana da dukiyoyi a Dubai

- Buratai ya ce iyalansa nada karfin arziki na mallakar dukiya a Dubai

- Buratai ya kara da cewa musanya ‘yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram shawarar na siyasa ne ba na sojoji bane

Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce iyalansa na da hannun jari a Dubai kafin a nada shi babban hafsan sojoji.

Buratai ya yi wannan magana ne a wani shiri na gidan rediyon BBC a ranar Talata, 4 ga watan Yuli, ya ce iyalansa ta zuba hannun jarin ne saboda tana da karfin arziki na mallakar dukiya a Dubai.

Buratai ya ce: "Na mallaki wannan dukiyar ne tun shekara 2013 kafin na yi tunani cewa zan zama babban hafsan sojoji, amma zai gashi a yanzu mutane na zargi na da ba dai dai ba kamar yanzu na saya dukiyar".

Ina da dukiya a Dubai kafin na zama hafsoshin soja – Inji Buratai

Laftanar Janar Tukur Buratai a lokacin da aka nada shi babban hafsan sojojin Najeriya Source: nationalhelm

NAIJ.com ta ruwaito cewa, a lokacin da yake magana a kan musanya ‘yan matan Chibok da fursunonin kungiyar Boko Haram, Buratai ya ce matakin an dauka ne a kan wasu bukatun kasar.

KU KARANTA: Ta'addancin Boko Haram ya sake leka Diffa ta Nijar

Ya ce: "Wannan ba shawarar mu bane, amma na siyasa".

A wani ci gaba kuma, babban hafsan sojan ya ce fiye da 700 'yan kungiyar Boko Haram suka mika wuya ga sojojin na Operation Lafiya Dole da ke Borno kuma ana san ran wasu kuma za su mika wuya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel