Za mu buga sunayen barayin gwamnati masu wawushe dukiyar kasa – Inji gwamnatin tarayya

Za mu buga sunayen barayin gwamnati masu wawushe dukiyar kasa – Inji gwamnatin tarayya

- Ministan shari'a, Abubakar Malami ya ce gwamnatin tarayya ta amince za ta buga sunayen barayin gwamnati wadanda suka wawushe dukiyar jama’a

- Malami ya ce gwamnati zata yi da’a ga hukuncin babbar kotun

- A ranar Laraba ne babbar kotun tarayyar da ke Legas ta umarni gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen wanda suka wawushe dukiyar jama’a

Gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli ta amince da buga sunayen barayin gwamnati wadanda suka wawushe dukiyar jama'an kasar kamar yadda babbar kotun tarayya da ke Legas ta umarni.

Ministan shari'a kuma babban lauyan na tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana hakan ne ga ‘yan jaridar fadar gwamnatin tarayya a ranar Laraba bayan zaman majalisar zartarwa.

A cewar Malami, gwamnatin tarayya ta amince da hukuncin da kotun ta yanke kuma zata bi, idan dai ba zai take hakkin dokoki na kotun.

KU KARANTA: Kotun ta umarni gwamnatin tarayya ta bayyana sunaye mutanen da suka wawushe arzikin Najeriya

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli ne babbar kotun tarayyar Najeriya da ke Legas ta umarni gwamnatin tarayya da ta bayyana wa ‘yan Najeriya sunayen jami'an gwamnati da kuma sauran mutane da suka wawushe dukiyar jama'ar kasar. Kotun ta kuma nema a bayyana ainihin adadin kudin da aka gano daga kowanen su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel