Dole Buhari ya yi murabus don amfanin Najeriya - Fayose

Dole Buhari ya yi murabus don amfanin Najeriya - Fayose

- Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya yi tambaya kan yadda kasa zata ci gaba alhalin shugabanta da tafiyar da mafi akasarin rayuwarsa a kasar waje don jinya

- Fayose ya tuna cewa ya daukaka wannan alámari na shekarun Buhari, lafiyarsa da ma tunaninsa a shekarar 2015

- Gwamnan ya yi kira ga Buhari da ya yi murabus kamar yadda shugabna kasar ya yi kira ga tsige YarÁdua a 2010

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya kuma kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus domin amfanin kasar.

A ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, Fayose ya buga shafinsa na twitter inda ya tambayi yadda zaáyi kasa ta ci gaba alhalin shugabanta na gudanar da yawancin rayuwarsa a kasar waje don jinya.

Dole Buhari ya yi murabus don amfanin Najeriya - Fayose

Dole Buhari ya yi murabus don amfanin Najeriya inji Fayose

Gwamnan ya tuna cewa ya yi Magana a kan shekarun Buhari, lafiyarsa da tunaninsa a shekarar 2015, sannan kuma ya yi gargadin cewa karda a zabe shi.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci zaman majalisa a yau, anyi shiru na minti guda ga Maitama Sule (hotuna)

Ya ce kawai Buhari ya ja gefe kamar yadda ya yi kira ga tsige Yar’Adua a 2010.

A halin da ake ciki, Fayose ya ce shi baya yi wa Buhari fatan mutuwa, shi fatan sa kawai ya ceto Najeriya daga na kewaye da fadar shugaban kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel