‘Yan fashi sun fitini mutanen Garin Zaria

‘Yan fashi sun fitini mutanen Garin Zaria

– Masu fashi da makami sun hana mutanen Zaria sakat

– Ko jiya dai an tare wasu a kan hanyar Zaria zuwa Kano

– Akwai bukatar Jami’an tsaro su kara maida hankali

Shekaran jiya Mutanen Samarun Zaria su ka wayi Gari da labari mai ban takaici na wani ‘Dan acaba da aka kashe a hanyar Shika. Haka dai aka iske gawar wannan mutumi nan a kwance.

‘Yan fanshi sun fitini mutanen Garin Zaria

Hotunan ‘Yan Sanda da wasu 'Yan fashi daga NAIJ.com

Da safiyar Ranar Talata dai ne mu ka ji labari daga wadanda ke zaune Garin Shika cewa 'Yan fashi sun yi ta'asa. A cikin daren Ranar Litinin kimanin karfe 12:00 zuwa 1:00 aka yi wani fashi. Kwanakin baya ma dai wasu ‘Yan fashi sun tare hanyar zuwa Garin Shikan.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kasa tsare wani na kusa da Jonathan

Haka kuma dai mutanen Garin Zabi da ke kan hanyar Kano su na cigaba da ganin fitina don kuwa masu fashi da makami sun hana hanyar sakat. Ko a jiya dai mun samu labari cewa an tare wasu a wurin.

Ku na da labari kwanan aka yi fashi daidai hanyar da ke kan Samaru zuwa Garin Shika. Sai Hukuma ta dage na domin kare lafiyar Jama'a.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za ka bar Kasar nan ka koma wata [Ga abin da mutane ke fada a bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel