Uwar-bari: Sanata Dino Melaye ya fara neman sauki

Uwar-bari: Sanata Dino Melaye ya fara neman sauki

– Sanata Dino Melaye ya nemi a ceci daga yunkurin kiranye

– Dino Melaye ya roki Sanatocin Najeriya su sa baki

– Hukumar zabe na kasa INEC dai ta kasa ta tsare

Kwanaki INEC ta aikawa Sanata Melaye takarda shirin kiranye. Tun nan Sanatan ya shiga fadi tashi. Dino Melaye ya nemi ‘Yan uwan sa su baki a lamarin. Tuni dai Shugaban Majalisar ya nuna cewa babu wanda ya isa ya kori Sanatan daga Majalisa.

Uwar-bari: Sanata Dino Melaye ya fara neman sauki

Melaye na gudun a tsige sa daga Majalisa Hoto daga NAIJ.com

Sanannen labari ne cewa Jama’ar Mazabar Yammacin Kogi na shirin maido Sanata Dino Melaye gida wanda har maganar ta kai ga Hukumar zabe na INEC. Hakan ta sa Sanatan ya zura Kotu da ya ga abin na yi ne.

KU KARANTA: Sanatoci za su tunbuke Osinbajo?

Uwar-bari: Sanata Dino Melaye ya fara neman sauki

Hoton yi wa Sanata Dino Melaye kiranye daga NAIJ.com

Dino Melaye ya kuma nemi ‘Yan uwan sa Sanatocin kasar su hana wannan yunkuri na yi masa kiranye kuma da alamu hakar sa na ci ma ruwa duk da Majalisa ba ta da wani iko. Haka kuma Jam’iyyar APC ta Jihar Kogi ta shiga Kotu domin hana ayi wa Sanatan na ta kiranye.

Idan ta tabbata lallai Dino zai bar Majalisar Dattawa babu wata-wata. Sai dai Hukumar INEC tace ba ta san da maganar Kotu ba kuma ba abin da zai hana ta wannan aiki na ta a yanzu haka.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko za ka iya barin Najeriya [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel