Majalisar Dattijai: Saraki ya caccaki wasu sanatoci a zaman ta na musamma

Majalisar Dattijai: Saraki ya caccaki wasu sanatoci a zaman ta na musamma

- Shugaban majalisar dattijai ya gargadi ‘yan majalisar da yin amo a lokacin zaman ta na musamma

- Saraki ya ce ko ‘yan majalisar su yi shurun ko su koma dakin shan shayi

- Shugaban majalisar musamman ya umarni sanata Kabiru Marafa cewa ko dai ya yi shurun ko ya koma dakin shan shayi

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Dr. Bukola Saraki a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli ya shawarci wasu sanatocin kasar da su daina yin amo a lokacin zaman ta na musamma.

Saraki ya bukaci wasu sanatoci cewa su koma dakin shan shayi idan ba zasu yi biyayya ga dokokin majalisar ba.

Wannan barazanar ta biyo bayan cecekucen ‘yan majalisar a lokacin da sanata Baba Kaka Garba ke bayar da nashi gudunmawa.

Majalisar Dattijai: Saraki ya caccaki wasu sanatoci a zaman ta na musamma

'Yan majalisar dattawan Najeriya Source: @NGRSenate

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta bukaci Fashola ya yi murabus

NAIJ.com ta ruwaito cewe jim kadan bayan jawo hankalin 'yan majalisar, shugaban majalisar musamman ya kira sanata Kabiru Marafa cewa ko dai ya yi shurun ko kuma ya koma dakin shan shayi idan bai da gudummawa a kan batun da ake magana a kan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel