Jirage 3 sun isa tashoshin jiragen ruwa da man fetur, da wasu kayayyakin abinci

Jirage 3 sun isa tashoshin jiragen ruwa da man fetur, da wasu kayayyakin abinci

- Wasu jirage sun isa tashoshin jiragen ruwa da ke Legas da man fetur da kuma wasu kayayyaki daban-daban

- A na san rai wasu jiragen ruwa 33 za su isa tashoshin jiragen ruwa tsakanin ranar Talata zuwa ranar 15 ga wata Yuli

- A yanzu haka jirage 24 ke sauke kayayyakin abinci daban daban

Jiragen ruwa guda uku sun isa tashoshin jiragen ruwa da ke Legas a ranar Talata, 4 ga watan Yuli da kayayyaki daban-daban, ciki har da man fetur. A cewar hukumar kula da tashshin jiragen ruwa, NPA.

Hukumar NPA ta bayyana hakan ne a wani kwafin takarda wanda aka samuwa kamfanin dilancin labarai, NAN, majiyar NAIJ.com a Legas .

Rahoton ta ce daya daga cikin jiragen na cike da taki.

Jirage 3 sun isa tashoshin jiragen ruwa da man fetur, da wasu kayayyakin abinci

Jiragen ruwa a tashoshin jiragen ruwa da ke Legas Source: today.ng

A cewar rahoton, a na san rai jiragen ruwa 33 dauke da man fetur da wasu kayayyakin abinci za su isa tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Tin-Can Island tsakanin ranar Talata zuwa ranar 15 ga wata Yuli.

KU KARANTA: Madalla! An fara sayar da takin zamani a farashi mai rahura a wannan jihar ta Arewa

Rahoton ta ci gaba da cewa yanzu haka wasu jiragen ruwa 24 suna sauke kayayyaki daban daban a tashoshin jiragen ruwa, ciki dar da alkama, gawayi, masara, gas, man fetur, daskararre kifi, dizal, kananzir da sauran su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel