Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 150 tare da asarar gidaje 1,233 a jihar Kros Ribas

Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 150 tare da asarar gidaje 1,233 a jihar Kros Ribas

An samu salwantar rayuka 150 a jihar Kros Ribas biyo bayan rikicin kabilanci daya barke a tsakanin jama’a wasu kauyuka biyu, da aka kwashe kwanaki 3 ana kai ruwa rana.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar, John Inaku yana bayyana cewa sama da mutane 14,000 ke gudun hijira a yanzu haka, baya an lalata gidaje 1,233.

KU KARANTA: Aiki sai mai shi: Yadda Ɗansanda yayi kwantan ɓauna a cikin lamba 2 yana dakon wani ɗan fashi (HOTO)

“A tsakanin 27 da 29 ga watan Yuni an samu rikicin kabilanci tsakanin al’ummar kauyukan Wanikade da Wanihem dukkaninsu a karamar hukumar Yala, inda aka lalata gidaje 1233, sa’annan an kashe mutane fiye da 150, da kuma fatattakar mutane 14,000 daga kauyukansu.” Inji shi.

Rikicin ƙabilanci ya laƙume rayuka 150 tare da asarar gidaje 1,233 a jihar Kros Ribas

Rikicin ƙabilanci a jihar Kros Ribas

Mista John yace a yanzu haka mutanen dake gudun hijira na tsugune a karamar hukumar Oju na jihar Benue, inda ya kara da cewa rikicin ya gurgunta al’amuran noma da da kasuwanci.

Sai dai Inaku yace gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Ben Ayade tare da hadin gwiwar cibiyar adanan abinci sun kai musu kayayyakin abinci daya hada da shinkafa, wake, gyada, man gyada da sauyransu.

Daga karshe, Inaku ya roki matasan dasu ajiye makamansu, tare da rungumar zaman lafiya, domin a cewarsa zaman lafiya yafi zaman dan Sarki.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Kaakakin rundunar yansandan jihar Irene Ugbo tana fadin tuni aka aika da jami’an tsaro domin kwantar da tarzomar tare da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda wata mata tayi asarar danta ga kungiyar asiri:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel