Kotun ta umarni gwamnatin tarayya ta bayyana sunaye mutanen da suka wawushe arzikin Najeriya

Kotun ta umarni gwamnatin tarayya ta bayyana sunaye mutanen da suka wawushe arzikin Najeriya

- Babbar Kotun tarayyar Najeriya ta umarni shugaba Buhari da Yemi Osinbajo da su bayyana sunayen barayin gwamnati ga ‘yan Najeriya

- Justice Hadiza Rabiu Shagari ta yake wannan hukunci biyo bayan karar da kungiyar SERAP

- SERAP ta ce ya zama wajibi a kan gwamnatin tarayya ta bayyana wa ‘yan Najeriya sunayen barayin gwamnati

Babbar kotun tarayyar Najeriya da ke Legas a yau Laraba, 5 ga watan Yuli ta umarnin gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu da ta bayyana wa ‘yan Najeriya sunayen jami'an gwamnati da kuma sauran mutane da suka wawushe dukiyar jama'ar kasar. Kotun ta kuma nema a bayyana ainihin adadin kudin da aka gano daga kowane.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Justice Hadiza Rabiu Shagari ta yake wannan hukunci a yau Laraba biyo bayan wani karar da kungiyar kare hakin bil adama wato Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta kai a kotun.

A shari'ar ta Justice Shagari ta amince da kungiyar SERAP cewa ya zama wajibi a kan gwamnatin tarayya ta bayyana wa ‘yan Najeriya sunayen wadanda ake zargi da wawushe dukiyoyin al’umman Najeriya.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta isa birnin Landan domin ganin mijinta

A cikin karar kungiyar ta na kuma tuhuma ministan labarai, Alhaji Lai Muhammed da ma'aikatar labarai da al'adu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel