Majalisar dattawa ta bukaci Fashola ya yi murabus

Majalisar dattawa ta bukaci Fashola ya yi murabus

- Sanata Danjuma Goje ya yi kira Babatunde Fashola da ya yi nuni da hali irin na minister ba wai gwamna ba

- Goje ya ce Fashola ya yi abun da ya kamata idan yana ganin tarin aikin dake ma’aikatar ayyuka ya sha kansa

- Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa Ibrahim Magu bai cancanci shugabancin hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFFC) ba

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje Babatunde Fashola (SAN) da ya yi murabus idan ya damu da yawan ayyuka dake ma’aikatar sa.

Shugaban kwamitin kula da dace na majalisar dattawa, Sanata Danjuma Goje, ya yi wannan kira a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, a martani ga furucin Fashola inda ya kalubalanci ‘yan majalisa kan canza akalar ayyukan ma’aikatar aiki a kasafin 2017.

Sakamakon fusata da tayi da furucin Fashola majalisar dattawa ta zargi ministan da batar da jama’a da kuma shafa wa ‘yan majalisa bakin fenti kan kasafin 2017.

KU KARANTA KUMA: Ina da wani buri! Kalli bidiyon Maitama Sule yana magana kafin mutuwar shi

Sanata Danjuma Goje, ya yi wata magana a lokacin da suke zama cewa Fashola minister ne sannan kuma shi ba gwamna bane a yanzu don haka ya nuna hakan a kalamansa., jaridar Punch ta ruwaito.

A halin da ake ciki, Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi ta kudu ya bayyana cewa Magu bai cancanci zama shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki (EFCC) ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel