A kafa kwamitin likitoci don tabbatar da idan Buhari ba zai kai labara ba – Wata kungiya ta fada ma Osinbajo da Saraki

A kafa kwamitin likitoci don tabbatar da idan Buhari ba zai kai labara ba – Wata kungiya ta fada ma Osinbajo da Saraki

- An bukaci shugaban kasa Buhari ya yi jawabi ga kasar zuwa ranar Alhamis

- Kungiyar ta kuma yi kira da a kafa kwamitin likitoci domin sanin halin da lafiyar shugaban kasar ke ciki

Wata kungiya ta umurci mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da su kafa kwamitin likitoci don sanin ko shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai moru ba.

Kungiyar ta ce wannan ya fada a karkashin sashi na 144 cikin wani bangare na sashi 4 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kungiyar ta kuma ce ya zama lallai shugaban kasar ya yi jawabi ga kasar ta bidiyo a ranar Alhamis, a cewar Sahara Reporters.

A kafa kwamitin likitoci don tabbatar da idan Buhari ba zai kai labara ba – Wata kungiya ta fada ma Osinbajo da Saraki

Wata kungiya ta kalubalanci shugaba Buhari

KU KARANTA KUMA: Ina da wani buri! Kalli bidiyon Maitama Sule yana magana kafin mutuwar shi

Kungiyar ta ce idan shugaba Buhari ya ki aikata hakan, za’a shirya zanga-zanga a fadin kasar koma fiye da hakan.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa kimanin mutane miliyan uku sun gudanar ma shugaba Muhammadu Buhari gangami a Owerri, babban birnin jihar Imo .

Wata kungiya ce ta shirya gangamin domin yiwa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari godiya bisa jajircewar gwamnatin gurin yaki da rashawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel