Buhari ya yi kuskure a kan Nnamdi Kanu, Najeriya na iya tarwatsewa - Agbakoba

Buhari ya yi kuskure a kan Nnamdi Kanu, Najeriya na iya tarwatsewa - Agbakoba

- Wani babban lauya ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kuskure a kan Kanu

- Olisa Agbako ya ce da an sani ba’a chaji Kanu da laifin cin amanar kasa ba

- Ya ce da gwamnatin tarayya ta sani ta chaje a kan shirya taro da baya bisa ka’ida kawai

A ranar Talata, 4 ga watan Yuli, tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya Olisa Agbakoba ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da yin kuskure gurin kama shugaban kungiyar masu fafutukar neman Biyafara Nnamdi Kanu.

Agbakoba yayinda yake jawabi ga yan jarida a Lagas kan makomar Najeriya ya ce laifin cin amanar kasa da gwamnatin tarayya ta chaji Kanu a kai ne ya daukaka fafutukarsa.

Agbako ya ce da an sani ba’a chaji Kanu a kan laifin cin amanar kasa ba.

Buhari ya yi kuskure a kan Nnamdi Kanu, Najeriya na iya tarwatsewa - Agbakoba

Buhari ya yi kuskure a kan Nnamdi Kanu, Najeriya na iya tarwatsewa inji Agbakoba

Da yake watsi da al’amarin sake fasalin al’amuran kasar Najeriya, Agbakoba ya ce a kada kuri’ar raba gardama domin sanin makomar Biyafara.

KU KARANTA KUMA: Ina da wani buri! Kalli bidiyon Maitama Sule yana magana kafin mutuwar shi

Ya ce da gwamnatin tarayya ta sani ta chaje shi a kan laifin shirya taro da baya bisa ka’ida sannan kuma hakan ka iya rusa zaman lafiyar jama’a a Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com inda shugaban masu fafutukar Biyafara ke jawabi ga mabiyansa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel