Ina da wani buri! Kalli bidiyon Maitama Sule yana magana kafin mutuwar shi

Ina da wani buri! Kalli bidiyon Maitama Sule yana magana kafin mutuwar shi

Anyi jana’izar marigayi Maitama Sule, Dan masanin Kano. Babban limamin Kano, Farfesa Sani Zaharaddeen, ne ya gabatar da sallar gawar da misalin karfe shidda da minti takwas na yamma (6:08pm), tare da Gwamna Abdullahi Ganduje da mataimankin sa, Farfesa Hafiz Abubakar da kuma sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II.

A yanzu haka ýan Najeriya da dama dake jimamin mutuwar ministan man fetur na farko, Maitama Sule, sun yi dan takaitaccen tarihin rayuwarsa don nuna cewa bashi da son zuciya idan aka zo gurin fadar gaskiya.

Dayawa daga cikin masu jimamin nasa kamar irin, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa Alhaji Sule ya rasu a lokacin da ake matukar bukatarsa saboda kwarewarsa da kuma mutuncinsa mussaman a yanzu da hadin kan Najeriya ke ci gaba da rawa.

Amma kafin mutuwarsa, Sule ya yi Magana game da fafutuka da kungiyar IPOB ke yin a neman biyafara, inda yace yankin kudu maso gabas bazata taba cimma Biyafara ba.

Ina da wani buri! Kalli bidiyon Maitama Sule yana magana kafin mutuwar shi

Marigayi, Alhaji Yusuf Maitama Sule

KU KARANTA KUMA: Buhari zai iya mulkin Najeriya ko a keken Guragu yake – Tsohon Soja

Sule wanda ya rasu a kasar Masar a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli yana da shekaru 88 a duniya, ya ce Allah na son kasar Najeriya ta jagoranci yankin Afrika shiyasa ya akayi nasarar hade kasar.

Marigayi Maitama Sule ya fadi abubuwa da dama game da mafarkinsa a kan Najeriya kafin mutuwarsa. Wannan bidiyo da Bashir Ahmad mataimaki na musamman ga shugaban kasa Buhari a shafin zumunta ya yada, ya nuna wasu daga cikin abubuwan da ya ce:

Da yake Magana a kan arewa da kuma hadin kan Najerya, Maitama Sule ya ce:

A ko wani hali, ‘yan arewa basa tsoro, amma basa so ya kasance. Bana so kasar nan ta rabu saboda mu da muke Arewa bazamu iya tsayawa da kafafunmu ba. Na san abun da muke da shi a kasar sannan na san abun da muke da shi a Arewa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan hadin kan Najeriya:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Kasafin kudi: Za a kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa

Najeriya za ta kashe makudan Biliyoyi wajen jiragen saman Shugaban Kasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel