Sharhi: Yadda za'a iya kira Dino Melaye gida daga Majalisar dattijai

Sharhi: Yadda za'a iya kira Dino Melaye gida daga Majalisar dattijai

- Ana kokarin maido da Sanata Dino Melaye gida

- Iyayen gidansa na kokarin ceto shi

- Hukumar zabe ta ce ba ja da baya

Ana kiki-kaka kan batun tsigewa da koro Sanatan jihar Kogi gida, daga Majalisar Dattijai a Abuja, ko ya yaya hakan zai yiwu?

Hukumar zabe ta kasa INEC, ta fitar da jaddawalin yadda kiranyen Sanatan zai yiwu, bayan da aka sami saka hannun mutum sama da rabin masu zabe a mazabarsa ta Kogi West, masu niyyar dawo dashi gida.

A tsarin dimokuradiyya dai, idan aka tura wakili majalisa, ko ta jiha ko ta tarayya, tsaf za'a iya dawo dashi idan baya aikin da jama'arsa suka tura shi yayi. Hakan dai bai taba faruwa ba, a tarihin kasar nan.

Sharhi: Yadda za'a iya kira Dino Melaye gida daga Majalisar dattijai

Sharhi: Yadda za'a iya kira Dino Melaye gida daga Majalisar dattijai

A yanzu dai sharuddan da za'a cika na fara duba yiwuwar dawo da sanatan sun cika, inda aka sami sahalewar mutum dubu 188, cikin mutum dubu 300 da suka yi rajista a yankin.

Garzayawar Melaye kotu, da kuma sabon karin kwarin gwiwa da ya samu daga shugabancin majalisar, baya nuin ya tsallake. Cikin wata uku, za'a gama tantance masu saka hannun da jin menene korafinsu a kansa, da wakilcin sa.

Idan an gama, sai a sake kada zaben rafarandan, a sami masu rinjaye, in ya tsallake, fa-lillahil hamdu, in ya fadi, zai dawo gida fanko, sai a sake zabe babu shi.

KU KARANTA KUMA: Kuskuren Buhari kan Nnamdi Kanu

A shekarar 2005 ma dai an kusa dawo da dan majalisa dami wakiltar Plateau, Lalong, amma hukumar zabe ta Maurice Iwu da ta gudanar da zaben, ya tsallake da 70% na kuri'un.

Kotu dai na iya sama wa Dino mafita, haka ma majalisar, ana iya jan zancen har shekaru biyu, wanda kafin nan ya gama wa'adin mulkinsa, sai ya je ya nemi wani aikin kafin ya sha kunya.

Duk dai wanda aka tsige da wuya ya sake wata katabus a siyasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel