Ni ban baiwa Majalisar Kano cin hancin miliyan N100 ba - Inji Dangote

Ni ban baiwa Majalisar Kano cin hancin miliyan N100 ba - Inji Dangote

- Aliko Dangote ya fito yace zargin da ake masa na bada cin hanci ‘ba gaskiya bane

- Ana zargin ya bada cin hanci don a dakatar da binciken da ake wa masauratar Kano

- Mai Magana da yawunsa Tony Chiejina yace 'zargin abin kunya ne ga Dangote'

Attajirin dan Kasuwa Aliko Dangote ya fito yace zargin da ake masa na bawa majalisar Kano cin hanci domin tsaida bincike da ake wa masarautar Kano 'ba gaskiya bane.'

Binciken ma bashi da asali bare tushe. Mai Magana da yawunsa ne Tony Chiejina yace 'wannan zargin abin kunya ne ga Dangote.

Ni ban baiwa majalisar Kano cin hancin miliyan N100 ba - inji Dangote

Ni ban baiwa majalisar Kano cin hancin miliyan N100 ba - inji Dangote

Rahotanni su nuna cewa Dangote ya bawa Shugaban Majalisar Dokokin Jahar kano Alhaji Kabiru Alhassan Rurum N100m na cin hanci. Alhaji Rurum yayi murabus a ranar litinin don bada damar yin bincike kan zargin da ake wa Dangote na bada cin hancin, domin kare martabarsa.

KU KARANTA: Abinci taiki-taiki ya iso tekun Legas

Majalisar Dokokin Ta Jahar Kano ta dakatar da binciken da ake wa masarautar Kano a watan Jiya. Wanda mataimakin Shugaban Kasa Prof. Yemi Osinbajo da wasu mayan mutane a Najeriya suka shiga tsakani ta hanyar Gwamnatin Jahar Kano ba daga Majalisar Dokoki ba.

Majalisar Dokokin Jahar Kano ta kafa wani kwamiti wanda zai yi bincike akan zargin da ake wa Dangote. Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa kwamitin mutum biyar wanda zai binciki tsohon shugaban majalisa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel