Tsige Osinbajo: Abubuwa 4 da majalisar dattawa ta nema daga mukaddashin shugaban kasa

Tsige Osinbajo: Abubuwa 4 da majalisar dattawa ta nema daga mukaddashin shugaban kasa

A rahoton baya da NAIJ.com ta kawo, an bayyana cewa barazanar tsige mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo idan yaki cire Ibrahim Magu, shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), da majalisar dattawa ta yi ya zubar da kimarta a idanuwan wasu ýan Najeriya.

Bayan afkuwar alámarin, majalisar dattawa sunyi yunkurin nada Bukola Saraki a matsayin mukaddashin shugaban kasa domin maye gurbin Osinbajo yayinda shugaban kasar ke waje, amma hakan bai yiwu ba.

A halin yanzu, me majalisar dattawan ke bukata daga Osinbajo, kuma menene ainahin hujjojinsu? Majalisar dattawan Najeriya ta buga wasu bukatu a shafinta na Twitter.

Ga cikakken jerin abubuwan da suke so:

1. Majalisar dattawan ta dakatar da duk wasu al’amurran da suka shafi tabbatar da mukamai daga bangaren zartarwa kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasar har sai an bi dokar da tarayyar kasar ta gindaya.

2. Dole mukaddashin shugaban kasa ya yi biyayya ga kundin tsarin mulki da kuma hukunci da majalisar dokoki ta shimfida ta bangaren tabbatar da mukamai.

3. Dole mukaddashin shugaban kasar ya yi biyayya ga duk wani mukami da majalisa ta ki amincewa da shi.

4Sanata Marafa Kabir ya kara da cewa dole mukaddashin shugaban kasar ya janye furucin da yayi na cewa majalisar dattawa bata da ikon tabbatar da mukamai.

Menene ra’ayinku a kan wannan? Ga wasu daga cikin sharhi daga shafin zumunta kan bukatar majalisar.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai iya mulkin Najeriya ko a keken Guragu yake – Tsohon Soja

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com don jin ra’ayin ‘yan Najeriya game da hadin kan kasar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel