Ainihin cutar da tayi sanadiyyar ajalin Dan Masanin Kano - Inji babban dan sa

Ainihin cutar da tayi sanadiyyar ajalin Dan Masanin Kano - Inji babban dan sa

- Babban dan dan Masanin Kano ya fadi abun da yayisanadiyar ajalin mahaifin su

- Yace bugun zuciya ne ya same shi

- Yace ranar Asabar din da ta gabata ne ya tafi kasar Misra

Labarin da muke samu daga majiya mai tushe shine cewa cutar bugun zuciya ce tayi sanadiyyar ajalin dan masanin Kano Marigayi Yusuf Maitama Sule.

Mun samu labarin cewa babban dan marigayin Alhaji Mukhtari Maitama shine ya bayyana cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne dai mahaifin nasu ya fita zuwa Al-Qhira a can kasar Masar domin jinya.

Ainihin cutar da tayi sanadiyyar ajalin Dan Masanin Kano - Inji babban dan sa

Ainihin cutar da tayi sanadiyyar ajalin Dan Masanin Kano - Inji babban dan sa

NAIJ.com ta samu labarin cewa lokaciin da ya kai kasar ta Misra sunyi masa aune-aune tare da gano wasu ciwuwukan dake damun sa amma kafin su fara yi masa magani sai Allah ya karbi rayuwar sa.

Marigayin Alhaji Maitama Sule ya rasu ya bar 'ya'ya goma, maza 4 da mata 6 ya kuma bar mata daya.

Allah Ya ba shi baiwar iya magana kuma kowa na son ya saurare shi. Amma duk da haka bai yadda 'ya'yansa su yi girman kai ba dominsa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa

Duniya juyi-juyi: Yadda abokai da 'yan uwa suka yi burus da Jonathan a ranar haihuwar sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel