Bukola Saraki ya tasamma ceton Dino Melaye daga kiranye na al'ummarsa

Bukola Saraki ya tasamma ceton Dino Melaye daga kiranye na al'ummarsa

- 'Sanatoci su zo su cece ni' - inji Dino Melaye

- Majalisa zata yi agaji', inji Bukola Saraki

- 'Muna nan tare da kai', inji Sanatoci

A jiya ne dai hukumar zabe ta INEC ta saki jaddawalin yadda kiranyen da mutan Kogi West suke yi wa sanatansu Dino Melaye, ta yadda zata kaya. Sai dai, ko dare bayyi ba, sai ga martani daga majalisa, inda shugaban majalisa ya ce ai sam bama aikin hukumar bane yin kiranye.

Sanata Bukola Saraki dai, dama shine uba a siyasa ga shi Dino Melaye, kuma ana ganin yana da karfin iya hana kiranyen tasiri. Haka kuwa aka yi, inda ya ce ko ma menene, majalisar ta dattijai ita ce zata yi kalami na karshe kan batun.

Bukola Saraki ya tasamma ceto Dino Melaye daga kiranye na al'ummarsa

Bukola Saraki ya tasamma ceto Dino Melaye daga kiranye na al'ummarsa

Shima dai Sanata Dino Melaye, ya ce wannan ba aikin jama'aesa bane, bita da kulli ne kawai wai gwamnan Kogin Bello yake yi masa, inda ya kira majalisar da ta taimaka ta cece shi kar a mayar da shi gida fanko.

KU KARANTA: Jaruma ta caccaki masu bilicin

Mataimakin shugaban majalisa ma dai, Sanata Ike Ikweremadu, yayi tsokaci kan batun, inda yace wannan aiki bazai taba nasara ba.

Sanata Nwaobashi kuwa na PDP, cewa ma yayi a binciki inda hukumar INEC ta sami kudin aikin tsige Dino din, domin wai, ai majalisar bata ma baiwa INEC kudin aikin ba, a kasafin kudin bana.

Ya kuma kara da cewa, yadda hukumar ke azarbabin tafiyar da kiranyen, ya nuna akwai wani hannu da ke tafiyar da hukumar daga yan siyasa.

Ba'a dai san yadda zata kaya ba. inda kowanne bangare na da makudan kudi da zai iya kashe wutar gabansa, kuma an san harkar kasar nan dai akwai cin hanci da rashawa cikin tsakar dare.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel