Bana so Buhari ya mutu - Fayose

Bana so Buhari ya mutu - Fayose

- Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari fatan samun lafiya

- Fayose ya fada a bainar jama’a cewa baya son shugaban kasa Buhari ya mutu

Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya buga a shafinsa na twitter cewa baya so shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu amma kawai dai yana so Najeriya ta samu yanci daga nakewaye da fadar shugaban kasa.

Fayose ya ce: “Babu wanda ke da buri a mutuwar Buhari amma maimakon haka, muna burin ceto Najeriya daga wadanda ke bautar da kasar a yanzu."

A halin yanzu, NAIJ.com ta rahoto cewa Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya nace kan cewa lallai shugaban kasa Muhammadu Buhari na nan bai san inda kansa yake cewa wannan ne ya sa uwargidansa, Aisha ta koma Landan.

Bana so Buhari ya mutu - Fayose

Fayose ya ce baya fatan shugaba Buhari ya mutu

KU KARANTA KUMA: Buhari zai iya mulkin Najeriya ko a keken Guragu yake – Tsohon Soja

Buhari na birnin Landan inda yake jinya kuma sannan sau biyu Aisha na kai masa ziyara cikin kasa da makonni uku. Fayose ya ce komawar da Aisha tayi cikin gaggawa ya tabbatar da cewa ya yi gaskiya a lokacin da ya yi ikirarin cewa shugaban kasar bai san inda kansa yake ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan wasu tambayoyi da ta yi game da lafiyar shugaba Muhammadu Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya

Kungiyar Atishai ta kasa a Najeriya, tayi taronta na 2017 na kasa a jihar Ikko a makon jiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel